Gwamnatin Jihar Yobe ta bayyana ɗaukar matakan tsaro na musamman don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a lokacin bikin Sallar Azumi. Wannan mataki ya biyo bayan tattaunawar tsaro da Gwamna Mai Mala Buni ya gudanar tare da manyan jami’an tsaro a Fadar Gwamnatin Jihar dake Damaturu ranar Laraba.
Gwamna Buni, wanda Mataimakinsa, Idi Barde Gubana ya wakilta a wajen taron, ya jaddada muhimmancin ɗaukar matakan tsaro a lokacin bukukuwan sallah don tabbatar da zaman lafiya a jihar. Ya yaba wa hukumomin tsaro a ƙoƙarinsu wajen tabbatar da doka da oda, sannan ya nuna godiya ga sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma a kan gudunmawar da suke bayarwa wajen warware rikice-rikicen da ke faruwa a yankunansu.
- Sojoji Sun Daƙile Harin Jirgi Mara Matuƙi A Yobe
- ‘Yansanda Sun Kama Wasu Mutane 2 Da Ake Zargi Da Yi Wa Yarinya ‘Yar Shekara 12 Fyade A Yobe
Kwamishinan ‘Yansanda na Jihar Yobe, Abubakar Abdul Osun, ya tabbatar da cewa jami’an tsaro sun shirya tsaf domin tabbatar da cewa bikin sallah zai gudana cikin tsanaki. Haka kuma, Mai baiwa Gwamnan Shawara kan harkokin tsaro, Janar Dahiru Abdulsalam (Mai Ritaya), ya ƙaryata jita-jitar cewa Boko Haram sun umurci al’ummar ƙaramar hukumar Gujba su bar yankunansu. Ya tabbatar da cewa jami’an tsaro na aiki tukuru don tsare al’umma da dukiyoyinsu.
Gwamnatin Jihar Yobe tare da hukumomin tsaro sun tabbatar da cewa za a bayar da cikakken tsaro a duk faɗin jihar yayin bukukuwan sallah.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp