A baya bayan nan, firaministan Japan, Fumio Kishida, ya tattauna da sakatare janar na NATO Jens Stoltenberg, wanda ke ziyara a kasar. Inda bangarorin biyu suka zuzuta batun karfin sojin kasar Sin cikin sanarwar hadin gwiwa da suka fitar.
A cewar Fumio Kishida, Japan za ta shiga cikin kawancen NATO a yankin Asiya da Fasifik. Wannan na nufin cewa, wasu a Japan na neman janyo wasu daga wajen yankin, domin cimma muradunsu na kashin kai da kawo barazanar yaki da fito na fito a yankin Asiya da Fasifik.
Wannan zamani da ake ciki, ba zamani ne da Japan za ta iya yi wa makwabtanta kutse ta karfin tuwo ba. Japan na yau, ba ta da damar kauce hanya. Idan ‘yan siyasar kasar Japan na son janyo fitina cikin gida da kawo tsaiko a yankin Asiya da Fasifik, tabbas za a ga ba daidai ba. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha)