GCFR Janar Murtala Ramat Muhammad, tsohon shugaban mulkin sojin Nijeriya, wanda ya jagoranci hambarar da mulkin soja na janar Johnson Aguiyi-Ironsi a shekarar 1966, ya mulki Nijeriya daga watan Yulin 1975 har zuwa lokacin da aka kashe shi a ranar 13 ga Fabrairun 1976.
Ramat, Janar ne da ya yi fice a lokacin yakin basasa na Biafra.
- Ba Za Mu Lamunci Yunƙurin Haifar Da Tarzoma A Adamawa Ba – Fintiri
- Bangaren Samar Da Kaya Ko Aiwatar Da Ayyukan Hidima Da Ma’aikatan Kamfani Ke Yi Ya Fadada A Kasar Sin A Shekarar 2023
An haife shi a Kano, 8 Nuwamba 1938 ya fara aikin sojin Nijeriya ne bayan kammala Makarantar sojin Royal Military Academy, Sandhurst. Ya zama Birgediya Janar a shekarar 1971, yana da shekaru 33, ya zama daya daga cikin manyan hafsoshin sojan Nijeriya.
A ranar 13 ga Fabrairun 1976, Janar Muhammed akan hanyarsa da ya saba bi a titin George da ke kusa da Sakatariyar gwamnatin tarayya a Ikoyi Legas, da misalin karfe 8 na safe, acikin motarsa kirar Mercedes-Benz, sai ga wasu gungun sojoji wadanda suka yi yunkurin juyin mulki karkashin jagorancin Laftanar Kanar Buka Suka Dimka, suka fito daga wani gidan mai, suka yi wa motar kwanton bauna kan hanyarsa ta zuwa ofishinsa da ke Barracks Dodan, inda suka kashe shi.
Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Olusegun Obasanjo ne ya ci gaba da gudanar da mulki, wanda ya kammala shirin mika mulki ga farar hula ta hanyar mika mulki ga Shehu Shagari a ranar 1 ga Oktoban 1979.
Abubuwan da Janar Murtala ya aiwatar a tarihin Nijeriya, wasu bangare na yabawa matuka wasu kuma akasin hakan saboda yanayin Jagorancinsa. A jagorancinsa ya yi amfani da karfin mulkin soji, tattalin arzikin kasa ya habaka, wanda ya kara inganta rayuwa a Nijeriya.