Babban taron hukumar kiwon lafiya ta duniya WHA karo na 77 na jiya Litinin, ya yanke shawarar kin amincewa da shigar da daftarin shirin da wasu kasashe suka gabatar a cikin ajandar taron, inda kasashen suka nemi a shigar da yankin Taiwan cikin taron bisa matsayin mambar sa ido.
Game da hakan, wakilin dindindin na kasar Sin a ofishin MDD dake birnin Geneva, da sauran kungiyoyin kasa da kasa a Switzerland Chen Xu, ya bayyana a taron manema labarai cewa, babban taron ya ki amincewa da shirin a tsawon shekaru 8 a jere, wanda hakan ya shaida cewa, yunkurin ware Taiwan daga kasar Sin ba zai cimma nasara ba, kuma ba za a siyasantar da batun yankin Taiwan a babban taro ba, kana ko shakka babu duk wani mataki da ake dauka, ko za a dauka zai ci tura.
A dai jiyan, mai magana da yawun ofishin kula da harkokin yankin Taiwan a majalisar gudanarwar kasar Sin Chen Binhua, ya jaddada kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, kuma Taiwan wani sashi ne na kasar Sin. Ya ce yadda babban taron ya yi watsi da daftarin shirin ya nuna cewa, kasashen duniya na nacewa ka’idar “kasar Sin daya tak a duniya” ba tare da tangarda ba. (Amina Xu)