• English
  • Business News
Friday, October 17, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yunkurin Taiwan Na Halartar Babban Taron WHO Bai Yi Nasara Ba Har Sau 8

by CGTN Hausa
1 year ago
Taiwan

LABARAI MASU NASABA

Sin Da Afrika Sun Yi Alkawarin Tabbatar Da Nasarar Shirin TVET Na Nahiyar Afrika

Xi Ya Taya Hukumar FAO Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwa

An kammala rajistar halartar babban taron hukumar kiwon lafiya ta kasa da kasa WHO karo na 77 a ranar 13 ga wata. Kuma an ki amincewa yankin Taiwan na kasar Sin ya halarci taron, lamarin da bai wuce zaton mutane ba. Yunkurin mahukuntan jam’iyyar Democratic Progressive Party wato DPP na halartar taron bai yi nasara ba har sau 8. Wannan ya nuna cewa, kasa da kasa sun cimma matsaya daya kan ka’idar “kasar Sin daya tak a duniya”. Yadda kasar Amurka ta goyi bayan yunkurin mahukuntan jam’iyyar DPP, da neman goyon baya ta hanyoyi daban daban da mahukuntan jam’iyyar DPP su ka yi, ya yi kama da wasan yara da ba ya jan hankali.

Yankin Taiwan bai samu iznin gwamnatin tsakiyar kasar Sin na halartar babban taron WHO ba. Babu kujerarsa a babban taron. Bisa muhimman ka’idojin da aka tanada cikin kudurin babban taron MDD mai lamba 2758 da kudurin babban taron WHO mai lamba 25.1, gwamnatin jamhuriyar jama’ar kasar Sin, ita ce halaltacciyar gwamnatin da ke wakiltar Sin daya tak a duniya, wadda ke da cikakken ikon mulkin kasa cikin tsarin MDD.A matsayinsa na wani lardin kasar Sin, an bai wa yankin Taiwan damar tattauna batutuwa masu ruwa da tsaki a babban taron WHO, bisa ka’idar “kasar Sin daya tak a duniya”.

Haka kuma, dalilin da ya sa Amurka ta dauki shekaru da dama tana mara wa Taiwan baya wajen halartar babban taron WHO, shi ne domin wasu ‘yan siyasar Amurka suna son yin amfani da Taiwan don daukar ra’ayin rikau kan kasar Sin a shekarar bana, inda za a gudanar da babban zaben shugaban Amurka. Ban da haka kuma, Amurka tana son taimakawa Taiwan halartar babban taron WHO don kalubalantar ka’idar “kasar Sin daya tak a duniya”, ta yadda za a juya wannan ka’idar don ta da hargitsi. (Tasallah Yuan)

 

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sin Da Afrika Sun Yi Alkawarin Tabbatar Da Nasarar Shirin TVET Na Nahiyar Afrika
Daga Birnin Sin

Sin Da Afrika Sun Yi Alkawarin Tabbatar Da Nasarar Shirin TVET Na Nahiyar Afrika

October 16, 2025
Xi Ya Taya Hukumar FAO Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwa
Daga Birnin Sin

Xi Ya Taya Hukumar FAO Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwa

October 16, 2025
Gaza
Daga Birnin Sin

Wane Ci Gaba Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Gaza Ta Haifar?

October 16, 2025
Next Post
Biyan Tukuici: Gwamna Yusuf Ya Ƙaddamar Da Tallafin Naira 50,000 Ga Mata 5,200 Duk Wata A Kano

Biyan Tukuici: Gwamna Yusuf Ya Ƙaddamar Da Tallafin Naira 50,000 Ga Mata 5,200 Duk Wata A Kano

LABARAI MASU NASABA

Ƙungiyar NNYLF Ta Gargaɗi Atiku Da Sowore Kan Cinna Wutar Rikici A Nijeriya

Ƙungiyar NNYLF Ta Gargaɗi Atiku Da Sowore Kan Cinna Wutar Rikici A Nijeriya

October 17, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Dalilin Karyewar Farashin Kayan Abinci

Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Dalilin Karyewar Farashin Kayan Abinci

October 17, 2025
Tinubu

Batun Yin Afuwa Ga ‘Yan Yankin Ogoni Huɗu

October 17, 2025
Shettima

‘Yan Nijeriya Na Dab Da Fita Daga Halin Kuncin Talauci – Shettima 

October 17, 2025
Manzon Allah

Manzon Allah (SAW) Ne Ya Kafa Tushen Wayewar Kai A Duniya

October 17, 2025
An Kashe Mutane Da Dama Da Kone Gidajensu A Wani Hari Da Aka Kai Benuwai

Yadda ‘Yan Bindiga Ke Zafafa Hare-hare A Jihohin Arewa Maso Yamma

October 17, 2025
Shugaban Najeriya Ya Kaddamar Da Aikin Samar Da Ruwa Da Kamfanin Sin Ya Gudanar A Birnin Abuja

Afuwar Tinubu Ga Masu Manyan Laifuka: Ta Bar Baya Da Ƙura

October 17, 2025
Tsohon Ɗan Majalisar Bayelsa Ya Shawarci Jonathan Ya Guji Neman Takara A 2027

Tsohon Ɗan Majalisar Bayelsa Ya Shawarci Jonathan Ya Guji Neman Takara A 2027

October 17, 2025
Sin Da Afrika Sun Yi Alkawarin Tabbatar Da Nasarar Shirin TVET Na Nahiyar Afrika

Sin Da Afrika Sun Yi Alkawarin Tabbatar Da Nasarar Shirin TVET Na Nahiyar Afrika

October 16, 2025
NAWIA

Ranar Abinci Ta Duniya: NAWIA Ta Tallafawa Mata 114  Da Kayan Aikin Gona A Zamfara

October 16, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.