Zaɓaɓɓen gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana alhininsa game da gobarar da ta tashi a shagunan shahararriyar kasuwar wayar salula da ke Bebeji Plaza a Gusau, babban birnin jihar.
Lamarin dai ya faru ne a daren ranar Litinin, inda ta lalata ƙadarori na miliyoyin Naira.
Da yake jawabi ga shugabannin kasuwar da kuma waɗansu daga cikin waɗanda abin ya shafa a yayin ziyarar da ya kai wurin a ranar Talata, Lawal ya jajanta wa masu sayar da wayoyin salular da kuma masu ƙadarorin waɗanda tabbas suka yi asarar da ba za a iya tantancewa ba sakamakon gobarar.
A wata takardar manema labarai da ofishin zaɓaɓɓen gwamnan ya fitar mai ɗauke da sa hannun Sulaiman Bala Idris, Lawal ya yi addu’ar Allah ya tsayar da dukkanin wani abu mara daɗi da zai zo a nan gaba.
“Muna wannan ziyarar ne domin nuna tausayawa da jajantawa duk waɗanda wannan bala’in gobara ya shafa kai tsaye a daren jiya.
“Na yi baƙin ciki da ɓarkewar wannan gobara ta tarwatsa shaguna tare da lalata dukiyoyi na miliyoyin Naira.
“Ɓarnar da wannan gobara ta haifar ya yi yawa. Na tantance wurin da abin ya faru kuma zan yi nazarin hanyoyin da za a bi na taimaka wa waɗanda abin ya shafa.
“Asarar da ta auku ba a taɓa yin irin ta ba. Ina roƙon Allah (SWT) ya bai wa waɗanda abin ya shafa ƙwarin gwuiwar jure wannan rashin. Ina kuma roƙon Allah da ya tsayar mana da duk wani bala’i irin wannan.”