Mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna, Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe, ta yi alkawarin inganta rayuwar al’ummar karkara, yayin da ta kaddamar da yakin neman zabe a karamar hukumar Jaba gabanin zaben kananan hukumomin jihar a ranar 19 ga watan Oktoba.
Dakta Sabuwa, a wajen gangamin yakin neman zaben, ta bukaci al’ummar yankin da su zabi Larai Sylvia Ishaku ta jam’iyyar APC mai mulki a matsayin shugabar karamar hukumar.
- Gwamnatin Kaduna Ta Raba Wa Manoma Taki Buhu 120,000
- Gwamna Sani Zai Kaddamar Da Cibiyar Kula Da Cutar Kansa Mai Gadaje 300 A Kaduna – Kwamishina
Ta kuma bada tabbacin ci gaba da ayyukan more rayuwa a karkara da Gwamnatin Sanata Uba Sani ke yi cikin hanzari, idan har aka zabi dukkan ‘yan takarar shugabannin kananan hukumomi da kansilolin APC a shiyyar baki daya.
A nata jawabin, ‘yar takarar shugabancin karamar hukumar Jaba, Larai Sylvia Ishaku, ta yabawa al’ummar karamar hukumar Jaba bisa goyon bayan da ta samu da amincewarsu da ita, inda ta yi alkawarin gudanar da ayyukan more rayuwa idan har aka zabe ta a matsayin shugabar karamar hukumar Jaba a zaben da za a yi a ranar 19 ga watan Oktoba.