Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Zamfara, (ZASIEC) Bala Aliyu Gusau ya bayyana Jam’iyyar PDP a matsayin wacce ta lashe zabe a jihar.
PDP ta lashe dukkanin kujerun da aka fafata a zaben da aka gudanar ranar Asabar a Jihar.
- Rarara Bai Kawo Kudin Aurena Ba – Aisha Humaira
- An Kaddamar Da Tsarin Taswirar Sinanci Da CMG Ya Baiwa Dakin Adana Kayan Tarihin Larco Na Peruø
Ya ce, jam’iyyar PDP ta bi ka’idojin doka kuma ta samu kuri’u mafi yawa, inda ya ce jam’iyyar ta lashe dukkanin kujerun kananan hukumomin jihar.
Gusau ya bai wa daukacin zababbun shugabannin da suka yi nasara takardar shaidar cin zabe.
Duk da cewa jam’iyyar bata shiga zaben ba, jam’iyyar APC ta yi tasiri sosai a zaben inda ta samu kuri’u da dama.