An fara gudanar da zaɓen cike gurbi na majalisar dokokin jihar Adamawa cikin kwanciyar hankali a ƙaramar hukumar Ganye, inda kayan zaɓe suka iso da wuri, kuma tantancewa da kaɗa ƙuri’a suka fara a lokaci guda a rumfunan zaɓe da dama.
Jami’an hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) sun gudanar da aikin tantance masu zaɓe a wurare da dama, inda aka samu taron jama’a tun da wuri a rumfunan Fadar Gangwari, da Sanga-sumi, da Kangaraso, da kuma Anguwan Leko.
- INEC Ta Gargaɗi Ƴan Siyasa Kan Azarɓaɓin Yaƙin Neman Zaɓen 2027
- Gwamnonin Nijeriya Sun Yi Ta’aziyyar Waɗanda Suka Rasu A Ambaliyar Ruwa A Adamawa
Zaɓen ya biyo bayan rasuwar tsohon ɗan majalisar dokokin jihar, Hon. Abdulmalik Jauro Musa na jam’iyyar APC, wanda yake wakiltar mazabar Ganye a majalisar.
Sai dai duk da haramcin zirga-zirga da aka saka, an lura da wasu ƴan kasuwa suna buɗe shaguna a kasuwar Doya, yayin da aikin zaɓe ke ci gaba da gudana lafiya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp