Hukumar jami’an tsaro ta farin kaya (DSS) ta Kama wani jami’in Jam’iyyar PDP mai suna Shehu Fatange Da kudi Naira miliyan 30, inda ta zarge shi da yunkurin sayan kuri’a.
Shehu Fatange, an kama shi ne a wani Otel yana raba kudaden ga wasu ‘ya’yan jam’iyyar a mazabar dan majalisar Chikun da Kajuru a yayin zaben cike gurbi da ake gudanarwa a yau asabar.

Majiyarnu ta tabbatar da cewa, jam’ian hukumar sun kama Fatange ne ranar juma’a dauke da makudan kudade, inda ta yi zargin cewa, wannan kudade na sayen kuri’u ne.

Hukumar ‘yansandan jihar Kaduna, ta bakin kakakinta, DSP Mansir Hassan, ya tabbatar da faruwan lamarin inda yace yanzu haka Fatange yana hannunsu domin ci gaba da bincike














