Gwamnatin jihar Kaduna ta sake jaddada kudirinta na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa gabanin zaben da za a yi a ranar 16 ga watan Agusta.
A yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa, kwamishinan yada labarai, Ahmed Maiyaki da kwamishinan kananan hukumomi da masarautu Sadiq Mamman Legas, sun bayyana zargin da hadakar kungiyar ADC karkashin tsohon Gwamna Malam Nasiru Elrufai ta yi a matsayin wani yunkuri na kawo cikas ga gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali.
- Salon Zamanantarwa Na Sin Kyakkyawan Misali Ne Ga Kasashen Afirka
- ‘Yan Sama Jannatin Shenzhou-20 Za Su Gudanar Da Zagaye Na 3 Na Aiki A Wajen Cibiyar Binciken Sararin Samaniya Ta Sin
A cewar kwamishinonin, INEC ce ke da alhakin gudanar da zabe tare da ba da tabbacin bayar da gudunmuwar kason su a matsayin masu ruwa da tsaki wajen ganin an gudanar da zabe cikin gaskiya da adalci.
Ahmed Maiyaki da Sadiq Mamman Legas a madadin gwamnatin jihar Kaduna sun ce ofishin babban lauyan gwamnati da kwamishinan shari’a zai yi nazari kan kalaman da kungiyar hadaka ta ADC ta yi tare da baiwa gwamnatin jihar shawara kan mataki na gaba.
Tun da farko a wani taron manema labarai, jam’iyyar African Democratic Congress da hadin gwiwarta sun zargi gwamnatin jihar Kaduna da daukar hayar ‘yan baranda sama da 4000 tare da cire naira miliyan 30 daga asusun kowace karamar hukuma domin kawo cikas ga zaben da ke tafe.Wannan shi ne bayanin da mataimakin shugaban jam’iyyar ADC na kasa reshen Arewa maso Yamma, Jafaru Ibrahim Sani da Shugaban Jam’iyyar na Jihar Kaduna Patrick Ambut.
A cewarsu, sun aika da koke ga INEC da hukumomin tsaro dangane da hakan.Wannan shi ne bayanin da mataimakin shugaban jam’iyyar ADC na kasa reshen Arewa maso Yamma, Jafaru Ibrahim Sani da Shugaban Jam’iyyar na Jihar Kaduna Patrick Ambut.
A cewarsu, sun aika da koke ga INEC da hukumomin tsaro dangane da hakan.ugaban jam’iyyar ADC na kasa reshen Arewa maso Yamma, Jafaru Ibrahim Sani da Shugaban Jam’iyyar na Jihar Kaduna Patrick Ambut.
A cewarsu, sun aika da koke ga INEC da hukumomin tsaro dangane da hakan.