Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ta bayyana Yakubu Adamu na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar Birnin Kudu/Buji a majalisar tarayya da aka gudanar ranar Asabar.
Kotun daukaka kara ta ce, a watan Nuwamba 2023, ta bayyana zaben 18 ga Maris, 2023 a mazabar Birninkudu/Buji a matsayin wanda bai kammalu ba, ta kuma ba da umarnin sake zabe a rumfunan zabe takwas.
- Zaben Cike Gurbin Makera: ‘Yan Takara Sun Yi Wa Liman Mubaya’a
- INEC Ta Dakatar Da Sake Zabe A Kano, Enugu, Akwa Ibom Sakamakon Ayyukan ‘Yan Daba
Bakwai daga cikin rumfunan zabe na karamar hukumar Birnin Kudu da daya kuma daga Buji.
Da yake bayyana sakamakon zaben, jami’in zaben, Farfesa Ahmad Baita, ya ce, Adamu na PDP ya samu kuri’u 43,053, yayin da Magaji Da’u na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 42,544.
Baita ya bayyana cewa, kuri’un da kowane dan takara ya samu a zaben cike-gurbin an kara da su ne akan zaben da aka yi a ranar 18 ga Maris, 2023 domin tantance wanda ya yi nasara.
“Adamu Yakubu na PDP, bayan ya cika sharuddan doka, an bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara ya kuma zama zababbe,” Cewar Baita.
Da yake mayar da martani kan nasarar da ya samu, Yakubu ya bayyana godiyarsa ga al’ummar mazabar guda takwas da abin ya shafa da daukacin mazabar da suka jaddada goyon bayansu gare shi.
Ya yi alkawarin yin abunda ya da ce kan nasarorin da ya samu a baya da ta yanzu da aka sake tabbatar masa.