Rundunar ‘yansandan Jihar Kano ta gurfanar da mutane 333 da ake zargi a gaban kotuna daban-daban, bisa laifukan da suka aikata a lokacin zaɓen cike gurbi da aka gudanar a mazaɓun Ghari da Tsanyawa da kuma Bagwai da Shanono.
Kwamishinan ‘yansanda jihar, Ibrahim Adamu Bakori, wanda ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a ranar Litinin, ya ce an kama waɗanda ake zargin ne bisa laifin kawo hargitsi a lokacin zaɓen.
- Akpabio Ya Ƙaryata Jita-jitar Ba Shi Da Lafiya
- Idan Jonathan Ya Tsaya Takara A 2027, Girmansa Zai Faɗi – Shehu Sani
Kayan da aka samu daga hannun waɗanda ake zargin sun haɗa da bindiga ɗaya ƙirar ‘pump-action’, bindigogi biyar na gargajiya, sanduna 94 da takuba 16 da adduna 18 da barandami 33 da wuƙaƙe 18.
Sauran abubuwan da aka kama sun haɗa da motoci 14 da akwatunan zaɓe biyu da ƙuri’un da aka riga aka jefa 163 da kuma kuɗi sama da Naira miliyan huɗu (N4m).
Daga ƙarshe kwamishinan ya kuma buƙaci mazauna Kano da su ci gaba da bin doka da oda, su ba da haɗin kai ga jami’an tsaro.
Ya kuma buƙace su da su ɗauki tsaro a matsayin nauyi na haɗin gwiwa, inda ya nanata cewa rundunar za ta ci gaba da kare martabar tsarin dimokuraɗiyya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp