A ranar Juma’a, 12 ga Mayu, 2023 Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta kafe sunayen ‘yan takarar da za su fafata a zaɓuɓɓukan gwamna na cike girbi da za a yi a jihohin Bayelsa, Imo da Kogi.
Hukumar ta yi kira ga jama’a da su yi wa sunayen karatun ta-natsu domin gano idan wani ɗan takara ya ba da bayanin bogi game da kan shi domin ɗaukar mataki.
Babban Kwamishina kuma shugaban kwamitin wayar da kan jama’a kan al’amurran zaɓe na INEC, Mista Festus Okoye, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa ga manema labarai da ya rattaba wa hannu.
A ranar 25 ga Oktoba, 2022 ne dai hukumar ta fitar da jadawalin ayyuka da tsare-tsaren da za a aiwatar a zaɓuɓɓuka uku na cike gurbi na gwamnonin jihohin waɗanda za a gudanar a ranar Asabar, 11 ga Nuwamba, 2023.
Jam’iyyun siyasa sun gudanar da zaɓuɓɓukan fidda gwani kamar yadda doka ta tanada, kuma sun wallafa sunayen ‘yan takarar su da mataimakan su tare da bayanan su a gidan yanar da hukumar ta tanada domin ɗora irin waɗannan hotunan da bayanan kafin wa’adin karfe 6 na yamma na ranar 5 ga Mayu ya cika.
Dukkan jam’iyyu 18 sun zaɓi ‘yan takarar su na zaɓen gwamnan Jihar Kogi, kuma jam’iyyu 17 ne su ka yi hakan a Imo da Bayelsa.
Mista Okoye ya tunatar da cewa dukkan jam’iyyun siyasa da za su shiga waɗannan zaɓuɓɓuka guda uku sun cike fom mai lamba EC9 mai ɗauke da cikakkun bayanan ‘yan takara da daftarin rantsuwa a kotu da kuma Fom EC9B mai ɗauke da jerin sunayen ‘yan takarar su.
Ya ce: “Kamar yadda sashe na 29 (3) na Dokar Zaɓe ta 2022 ya tanadar, hukumar za ta wallafa sunaye da bayanan ‘yan takarar a ofisoshin ta na hedikwatar jihohin uku da ƙananan hukumomin su a ranar Juma’a, 12 ga Mayu, 2023.
“Mu na kira ga ‘yan Nijeriya da su karanta bayanan da kyau. Musamman mu na so duk wani ɗan takara da ya shiga zaɓen fidda gwani na jam’iyyar idan ya ga wani bayani da ya tabbatar na ƙarya ne da wani ɗan takara ya bayar, ya na iya shigar da ƙara a Babbar Kotun Tarayya kamar yadda sashe na 29(5) na Dokar Zaɓe ta 2022 ya tanadar.”