• English
  • Business News
Monday, October 20, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Zaɓin Hanyar Ci Gaba Tare Ta BRICS Ya Ja Hankalin Duniya

by Sulaiman
2 years ago
BRICS

A makon jiya ne aka gudanar da taron ƙolin BRICS karo na 15 a ƙasar Afirka ta kudu inda aka samu ƙarin ƙasashe da suka nuna shawarar zama mambobin ƙungiyar bayan tabbatar da shigar ƙasashen Habasha, da Masar, da Argentina, da Saudiyya, da Iran da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa cikin ƙungiyar. 

A halin yanzu, duniya ta fahimci cewa, BRICS ba ƙungiyar siyasar hada-hadar kuɗi ta yau da kullun ta duniya ba ce, kuma ba neman maye gurbin tsarin tattalin arzikin yammacin duniya take yi ba. Manufarta wani yunƙuri ne na tallafawa ci gaban ƙasa da ƙasa da kuma taimakawa wajen gina tsarin mai daidaito a duniya ta hanyar inganta haɗin gwiwar ƙasashe masu tasowa da kuma ciyar da muradun ƙasashen duniya gaba tare.

  • Mai Magana Da Yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ya Ba Da Amsa Kan Fadada BRICS

Duk da cewa ƙorafe-ƙorafe da dama game da ayyukan cin zarafi na kasuwanci, da rashin daidaito tsakanin ƙasashen duniya, da matsin lambar siyasa da tattalin arzikin wasu al’ummomi, da rashin mutunta tsare-tsaren yarjejeniyar haɗaka da Amurka ke yi da kuma rashin kulawa da buƙatun ci gaban ƙasashe matalauta sun haifar da kiraye-kirayen “sake fasalin” tsarin hada-hadar kuɗi na ƙasa da ƙasa.

A yayin da waɗannan ƙasashen yamma ke muzguna wa ƙasashe masu tasowa, ita kuma BRICS ta mai da hankali a kan gina mambobinta tare da ƙirƙirar cibiyoyi na tattalin arziki kamar Sabon Bankin Raya Kasa (NDB) da Shirin Tanadin Gaggawa wato Reserve Contingent Arrangement (CRA). Ƙungiyar ta kafa waɗannan hukumomin biyu a cikin 2015 da nufin tattara albarkatu don samar da kuɗaɗen samar da ababen more rayuwa da ayyukan ci gaba mai ɗorewa a ƙasashe masu tasowa da samar da hanyar tsaro ga ƙasashe mambobin ƙungiyar a cikin yanayin ma’auni na daidaita matsin lamban bashi da a kan fuskanta daga ƙasashen yamma.

NDB na samun ci gaba ta wannan hanya yayin da ta fara ba da lamuni da kuɗaɗen cikin gida wadda take da niyyar kaiwa kashi 30 cikin ɗari cikin shekaru biyar masu zuwa. Fiye da ƙasashe 20 ne suka gabatar da takardar neman zama mambobin bankin daga ciki akwai Masar, da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Bangladesh waɗanda suka shiga a shekarar 2021. Ƙasar Uruguay ita ma tana kan hanyar kammala shirye-shiryen zama mamba. Ministan kuɗi na Afirka ta Kudu, Enoch Godongwana ya bayyana a farkon wannan wata cewa, haɓaka amfani da kuɗaɗen cikin gida, shi ma zai kasance cikin ajandar da za ta taimaka wajen dakile tasirin canjin kuɗaɗen waje.

LABARAI MASU NASABA

Binciken CGTN: An Fitar Da Sakamakon Jin Ra’ayin Jama’a Dangane Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Kolin JKS Na 20

Xi Jinping Ya Mika Sakon Taya Cheng Li-wun Murnar Zama Shugabar Jam’iyyar KMT Ta Kasar Sin

Bayanai daga bankin duniya sun nuna cewa, rahoton zuba jari na BRICS na MDD kan cinikayya da raya ƙasa a watan Afrilu ya bayyana cewa, kason BRICS a cikin GDPn duniya ya ƙaru da kashi 18 cikin ɗari a shekarar 2010 zuwa kashi 26 cikin ɗari a shekarar 2021, a sakamakon bunƙasuwar da ƙasar Sin ta samu. Har ila yau, ta ce yawan hannun jarin kai tsaye na shekara-shekara ya ninka sau hudu tsakanin shekarar 2011 zuwa 2021, tare da ƙaruwar yawan kayayyakin da ake fitarwa a cikin ƙasashen BRICS ya zarce matsakaicin jimillar da duniya ke samarwa. Don haka, BRICS ta taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa tattalin arzikin abokan tarayya kuma ta ba da gudummawa sosai ga “samuwar ƙayyadaddun jari.”

A shekarar 2021, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya gabatar da ra’ayin samun bunƙasuwa tare ta hanyar shirinsa na raya ƙasa da ƙasa. A karkashin shugabancin ƙasar Sin a shekarar da ta gabata, ƙasashen BRICS sun bibbiyi wannan tsarin da sauran shirye-shiryen raya haɗin gwiwa da suka hada da shirin BRICS kan cinikayya da zuba jari don ci gaba mai ɗorewa, da tsarin haɗin gwiwar tattalin arziki na dijital, da tsarin haɗin gwiwar sararin samaniya da cibiyar bincike da raya allurar rigakafi ta BRICS.

Shekarar 2023 ta kasance “shekara mafi tasiri” ta ƙungiyar. Yayin da ƙasar Afirka ta Kudu ta karbi ragamar shugabancin BRICS daga ƙasar Sin, alamu sun tabbatar da yadda ƙasar Sin ta ci gaba da mai da hankali da samun nasarar raya ci gaban duniya. Wani muhimmin al’amari na BRICS shi ne cewa kasashe hudu daga cikin mambobinta suna cikin ƙungiyar G20.

A cikin shekaru 15 da suka gabata, BRICS ta zama wani babban jigo a tattalin arziƙin duniya. Wannan haɗin gwiwa tsakanin ƙasashe masu tasowa, ya haifar da wata hanya ta tabbatar da adalci da na ƙasa da ƙasa da kuma samar da zaman lafiya a duniya tare da yin kira ga sauran ƙasashe masu ƙarfin fada a ji, da kokarin jefa duniya cikin rashin zaman lafiya, da su gyara hanyoyin da ba su dace ba. (Yahaya)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Binciken CGTN: An Fitar Da Sakamakon Jin Ra’ayin Jama’a Dangane Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Kolin JKS Na 20
Daga Birnin Sin

Binciken CGTN: An Fitar Da Sakamakon Jin Ra’ayin Jama’a Dangane Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Kolin JKS Na 20

October 19, 2025
Xi Jinping Ya Mika Sakon Taya Cheng Li-wun Murnar Zama Shugabar Jam’iyyar KMT Ta Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Xi Jinping Ya Mika Sakon Taya Cheng Li-wun Murnar Zama Shugabar Jam’iyyar KMT Ta Kasar Sin

October 19, 2025
Tie Ning Ta Halarci Bikin Bude Taron Karawa Juna Sani Na ‘Yan Majalisun Dokokin Kasashen Afirka
Daga Birnin Sin

Tie Ning Ta Halarci Bikin Bude Taron Karawa Juna Sani Na ‘Yan Majalisun Dokokin Kasashen Afirka

October 19, 2025
Next Post
Sin A Shirye Take Ta Yi Aiki Tare Da Sabuwar Gwamnatin Zimbabwe

Sin A Shirye Take Ta Yi Aiki Tare Da Sabuwar Gwamnatin Zimbabwe

LABARAI MASU NASABA

Kano Derby: Barau FC Ta Doke Kano Pillars A Karon Farko A Tarihin Gamuwarsu

Kano Derby: Barau FC Ta Doke Kano Pillars A Karon Farko A Tarihin Gamuwarsu

October 19, 2025
Binciken CGTN: An Fitar Da Sakamakon Jin Ra’ayin Jama’a Dangane Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Kolin JKS Na 20

Binciken CGTN: An Fitar Da Sakamakon Jin Ra’ayin Jama’a Dangane Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Kolin JKS Na 20

October 19, 2025
Arewa Ta Samu Kashi 56% Na Muƙaman Gwamnatin Tinubu — Shugaban FCC

Arewa Ta Samu Kashi 56% Na Muƙaman Gwamnatin Tinubu — Shugaban FCC

October 19, 2025
Xi Jinping Ya Mika Sakon Taya Cheng Li-wun Murnar Zama Shugabar Jam’iyyar KMT Ta Kasar Sin

Xi Jinping Ya Mika Sakon Taya Cheng Li-wun Murnar Zama Shugabar Jam’iyyar KMT Ta Kasar Sin

October 19, 2025
Ɗan Jarida Ibrahim Ɗan’uwa Rano Ya Shaƙi Iskar Ƴanci Bayan Tsare Shi

Ɗan Jarida Ibrahim Ɗan’uwa Rano Ya Shaƙi Iskar Ƴanci Bayan Tsare Shi

October 19, 2025
Tie Ning Ta Halarci Bikin Bude Taron Karawa Juna Sani Na ‘Yan Majalisun Dokokin Kasashen Afirka

Tie Ning Ta Halarci Bikin Bude Taron Karawa Juna Sani Na ‘Yan Majalisun Dokokin Kasashen Afirka

October 19, 2025
Ƴansanda Sun Kama Ɗan Jarida A Kano Bisa Zargin Ɓata Suna

Ƴansanda Sun Kama Ɗan Jarida A Kano Bisa Zargin Ɓata Suna

October 19, 2025
Amfanin Yawan Shan Ruwa Da Kuma Illolin Rashin Yawan Sha

Amfanin Yawan Shan Ruwa Da Kuma Illolin Rashin Yawan Sha

October 19, 2025
Xinjiang Ta Janyo Karin Jari A Rubu’i Uku Na Farkon Shekarar Nan

Xinjiang Ta Janyo Karin Jari A Rubu’i Uku Na Farkon Shekarar Nan

October 19, 2025
Yadda Shagwaɓa Kananan Yara Da Kudi Ke Shafar Tarbiyyarsu

Yadda Shagwaɓa Kananan Yara Da Kudi Ke Shafar Tarbiyyarsu

October 19, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.