Dan gwagwarmayar kare hakkin Dan’adam kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Dakta Sani Ahmad Zangina, ya nuna juyayi tare da alhini kan rasuwar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a ranar Lahadin da ta gabata a kasar Burtaniya sakamakon dogon jinya da ya yi.
Dakta Zangina ya bayyana hakan a wani sakon ta’aziyya na musamman da ya fitar, inda yake bayyana rasuwar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin wani tabo a zuciya, wanda ba zai taba warkewa ba.
Ya ce, “Lallai an mana rashi mai zafi, wannan babban gurbi ne a Nijeriya wanda ba zai taba cikewa. Buhari mutum ne mai dattako da tausayin talakawan, yau an wayi gari babu shi, lallai al’umma sun yi alhini domin kuwa babu wani irinsa a kasar nan.”
Zangina ya yi kira ga dukkan yan siyasa da su yi dubi zuwa ga rayuwar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda ya ce, “Baba Buhari ya tashi maraya bai ma san mahaifinsa ba, a wajen mahaifiyarsa ya tashi kafin nan ya shiga aikin soja, amma yau sunansa duk inda ka kira an san shi, kuma dai an san irin wahalar da maraya yake sha idan ya tashi babu mahaifinsa a rayuwa da zai taimaka masa, saboda haka kawai ka dogara ga Allah kan komai, Allah zai maka duk abunda kake bukata ba sai ka kauce hanya ba.
“Muna kallon Buhari a matsayin wani kwarzon da ya zo domin ya ceci talakawan Nijeriya daga halin da suke ciki na kunci da tashi hankali, amma dai ya yi iya bakin kokarinsa har ya sauka, saboda kowa zai iya shaidarsa a kan Buhari mutum ne mai gaskiya da rikon amana, mutum ne da Allah ya jarabce shi da ‘yan Nijeriya. A lokacin da ya samu mulki yana ganin za a samu sauki ga talakawa, amma wadanda suka cutar da shi, wadanda ya ba su amanar kasar wanda har yanzu muna kallo ana tuhumarsu kan badakaloli da daman gaske ciki har ma dan’uwansa da ya ba shi minista.
“Muna addu’a tare da fatan Allah ya gafarta wa Baba Buhari, ya sa ya huta,” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp