Taron manema labarai na ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ya bayyana a yau Alhamis cewa, za a gudanar da bikin Canton Fair karo na 136 daga ran 15 ga watan Oktoba zuwa ran 4 ga watan Nuwamba a birnin Guangzhou na Sin, kuma ana gudanar da shaguna masu alaka da bikin ta yanar gizo yadda ya kamata ko da yaushe.
Bisa labarin da aka gabatar, girman wurin da za a gudanar bikin ya kai kimanin fadin muraba’in mita miliyan 1.55, da shaguna dubu 74. Yawan kamfanoni da za su halarci bikin na zahiri ya zarce dubu 30, daga cikinsu yawan sabbin kamfanoni ya kai kimanin 4600. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp