A jiya Talata ne a birnin Shanghai, kwamitin bunkasuwa da gyare-gyare na kasar Sin, da ma’aikatar masana’antu da fasahar sadarwa, da kuma gwamnatin birnin Shanghai, suka gudanar da taron manema labarai cikin hadin gwiwa, kwanaki 30 sun ragu kafin bude taron fasahohin kwaikwayon tunanin bil adama na duniya na shekarar 2022 wanda zai gudana a birnin Shanghai.
Jigon taron na wannan karo shi ne “Taron fasahohin kwaikwayon tunanin bil adama na duniya na shekarar 2022, hade duniya ta fasaha ba tare da iyakoki ba”.
Kaza lika an tsara hada sabon tsarin masana’antu na sabuwar hanyar Shanghai, da nuna sabon ra’ayi, da sabon ci gaba, da kuma sabon sakamako mai nasaba da tattalin arzikin fasahar sadarwa.
Wannan taro yana da dandalin tattaunawa kimanin 100, wadanda suka shafi fannoni guda hudu, wato kirkirar fasaha, da aikace-aikacen masana’antu, da dokoki da gine-ginen muhalli, wadanda suka hada da batutuwa fiye da 30, da kamfanoni dake shiga ciki fiye da 150.
Za a gudanar da taron fasahohin kwaikwayon tunanin bil adama na duniya na shekarar 2022 a birnin Shanghai ne tsakanin ranar 1 zuwa 3 ga watan Satumba dake tafe. (Safiyah Ma)