Tawagar gwamnatin jihar Gombe karkashin jagorancin kwamishinan da ke sanya ido a ma’aikatar muhalli da gandun daji, Shehu Ibrahim Madugu, ta ziyarci wasu al’ummomin da ambaliyar ruwa ta shafa a garin Bajoga da ke karamar hukumar Funakaye.
Ziyarar ta’aziyya da tantance barnar da tawagar gwamnatin jihar ta kai ya biyo bayan umarnin da gwamna Muhammad Inuwa Yahaya, ya bayar ga ma’aikatar muhallin da hukumar bada agajin gaggawa ta jihar (SEMA) da hukumomin da abin ya shafa kan gaggauta ziyar tare da tantance irin barnar da ambaliyar ta yi, tare da bada tallafi ga wadanda ibtila’in ya shafa don saukaka musu radadi.
- NBC Ta Ci Tarar Trust TV Tarar Miliyan 5 Kan Yada Ayyukan ‘Yan Bindiga
- Yajin Aikin ASUU: Kungiyar Dalubai Ta Bukaci A Kori Ministan Ilimi
Sauran ‘yan tawagar gwamnatin jihar sun hada da kwamishinan tsaron cikin gida da kyautata tarbiyya, Adamu Dishi Kupto, da babban sakataren ma’aikatar muhalli, Ibrahim Sule Bage da wakilin hukumar bada agajin gaggawa (SEMA) da sauransu.
Tawagar ta samu tarba daga shugaban karamar hukumar Funakaye, Alhaji Ibrahim Cheldu da sauran masu ruwa da tsaki wadanda suka zagaya da su yankunan da lamarin ya shafa.
A jawabinsa yayin ziyarar, kwamishina Shehu Ibrahim Madugu, ya mika sakon ta’aziyya da jajantawa na gwamna Inuwa Yahaya, bisa asarar rayuka da dukiyoyi da ambaliyar ta shafa a karamar hukumar.
“Makasudin zuwanmu a yau shi ne mu jajanta tare da mika ta’aziyyarmu gare ku bisa wannan ibtila’in daya shafe ku, tare da tantance barnar da ambaliyar ta haifar da nufin bai wa gwamnati shawara don samar da tallafi ga wadanda lamarin ya shafa”.
Sai ya bukaci al’ummomin da ke fuskantar matsalar ambaliya su yi biyayya ga hasashen ambaliyar ruwa da gargadin da Hukumar Kula da Yanayi ta Nijeriya (NIMET) ta yi.
A nasa jawabin, shugaban karamar hukumar Funakaye, Ibrahim Adamu Cheldu, ya yaba wa gwamna Inuwa Yahaya, bisa umarnin gaggawa da ya bayar wajen taimaka wa wadanda abin ya shafa tare da bada tabbacin majalisarsa cewa a shirye take ta mara wa gwamnatin jihar baya a kowane lokaci.
Tawagar ta kuma ziyarci Mai Martaba Sarkin Funakaye, Alhaji Muazu Mohammed Kwairanga tare da jajanta masa bisa ibtila’in daya samu al’ummar tasa.
Idan za a iya tunawa wani yaro dan shekaru uku ya rasu yayin da dan uwansa dan shekaru biyu ya samu munanan raunuka sakamakon mamakon ruwan sama da ya yi barna a wasu yankunan garin Bajoga da suka hada da Shara-Mansur da Bodoriyel.
Yankunan da aka ziyarta sun hada da Shara Mansur, da Jillahi da dai sauransu.