ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, November 13, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Za A Gudanar Da Zaben Kananan Hukumomin Jihar Nasarawa A Watan Nuwamba

by Zubairu M Lawal
1 year ago
Zaben

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Jihar Nasarawa, ta sanar da ranar da za ta gudanar da zaben Kananan Hukumomi a jihar.

Da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa, Shugaban Hukumar, Barista Ayuba Wandai, ya ce za a gudanar da zaben a ranar 2 ga watan Nuwamba, 2024.

  • Tinubu Zai Yi Balaguro Zuwa Birtaniya Na Mako 2
  • Ka Da Mu Yanke Kauna Da Nijeriya – Jonathan

Wandai, ya ce; “Wa’adin shugabannin kananan hukumomin da aka zaba a shekarar 2021 ya kare.”

ADVERTISEMENT

Ya ce dokar zaben kananan hukumomi ta jihar da aka yi wa gyara a 2018 ta ba su damar u yi shekara uku ne a kujerar.

Ya ce sun tattauna da shugabannin jami’yyu da ke jihar kuma sun gamsu da tsare-tsarensu.

LABARAI MASU NASABA

Neman Gurbin Kofin Duniya: Nijeriya Ta Lallasa Gabon Da Ci 4

NDLEA Ta Ƙona Miyagun Ƙwayoyi Sama Da Kilo 52,000 A Kaduna

Ya ce; sun bayar da damar gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyu daga ranar Juma’a 11 zuwa Alhamis 17 ga watan Oktoba, 2024.

Sanan za a fara gudanar da yakin niman zabe daga ranar 18 ga watan Oktoba.

Haka kuma kowace jam’iyya da ta shiga zaben za ta mika sunayen ‘yan takararta a ranar 29 ga watan Oktoba.

Sannan a gudanar da zaben a ranar 2 ga watan Nuwamba.

Ya ce hukumar za ta sanar da duk sakamakon da ya zo teburrinta.

Cikin takardum ka’idojin zaɓen an sanya kudin sayan fom din takara na Shugabannin Kananan Hukumomi a kan Naira miliyan 2.5.

Na Kansila zai tashi a kan Naira miliyan daya kacal.

Haka zalika za a sauke sunan duk dan takarar da aka same shi a matsayin ma’aikacin Gwamnatin Tarayya ko ta jiha ko ta karamar hukumar da ya tsaya takarar ba tare da ya ajiye aikin ba.

Ya ce masu kada kuri’a za su kasance daga shekara 18 zuwa sama.

Kuma an tanadi matakan tsaro domin gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Neman Gurbin Kofin Duniya: Nijeriya Ta Lallasa Gabon Da Ci 4
Manyan Labarai

Neman Gurbin Kofin Duniya: Nijeriya Ta Lallasa Gabon Da Ci 4

November 13, 2025
NDLEA Ta Ƙona Miyagun Ƙwayoyi Sama Da Kilo 52,000 A Kaduna
Labarai

NDLEA Ta Ƙona Miyagun Ƙwayoyi Sama Da Kilo 52,000 A Kaduna

November 13, 2025
Jiga Jigan APC Sun Ziyarci Majalisar Wakilai Bayan Sauya Sheƙar Ƴan NNPP 2
Manyan Labarai

Jiga Jigan APC Sun Ziyarci Majalisar Wakilai Bayan Sauya Sheƙar Ƴan NNPP 2

November 13, 2025
Next Post
Zamanantarwa Irin Na Kasar Sin Za Ta Kawo Sabbin Damammaki Ga Duniya

Zamanantarwa Irin Na Kasar Sin Za Ta Kawo Sabbin Damammaki Ga Duniya

LABARAI MASU NASABA

Shugabar IOC: Gasar Wasanni Ta Kasar Sin Tana Da Babbar Ma’ana

Shugabar IOC: Gasar Wasanni Ta Kasar Sin Tana Da Babbar Ma’ana

November 13, 2025
Ayyukan Kirkire-kirkire Na Kamfanonin Sin Na Kara Zama Babbar Kadara Ga Duniya

Ayyukan Kirkire-kirkire Na Kamfanonin Sin Na Kara Zama Babbar Kadara Ga Duniya

November 13, 2025
Neman Gurbin Kofin Duniya: Nijeriya Ta Lallasa Gabon Da Ci 4

Neman Gurbin Kofin Duniya: Nijeriya Ta Lallasa Gabon Da Ci 4

November 13, 2025
An Gudanar Da Taro Mai Taken “Shugabancin Duniya: Ayyukan Matasa” A Johannesburg Dake Afirka Ta Kudu

An Gudanar Da Taro Mai Taken “Shugabancin Duniya: Ayyukan Matasa” A Johannesburg Dake Afirka Ta Kudu

November 13, 2025
Xi Ya Bukaci Matasa Masanan Harkokin Sin Su Kasance Gada Tsakanin Sin Da Duniya

Xi Ya Bukaci Matasa Masanan Harkokin Sin Su Kasance Gada Tsakanin Sin Da Duniya

November 13, 2025
Shugabannin Sin Da Comoros Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 50 Da Kafa Alakar Diplomasiyya Tsakanin Kasashensu 

Shugabannin Sin Da Comoros Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 50 Da Kafa Alakar Diplomasiyya Tsakanin Kasashensu 

November 13, 2025
Sanarwar Taron Ministocin Harkokin Waje Na Kungiyar G7 Ba Ta Da Tushe

Sanarwar Taron Ministocin Harkokin Waje Na Kungiyar G7 Ba Ta Da Tushe

November 13, 2025
NDLEA Ta Ƙona Miyagun Ƙwayoyi Sama Da Kilo 52,000 A Kaduna

NDLEA Ta Ƙona Miyagun Ƙwayoyi Sama Da Kilo 52,000 A Kaduna

November 13, 2025
An Kafa Cibiyar Kiwon Lafiya Ta Hadin Gwiwa Ta Farko Tsakanin Sin Da Afirka A Guinea

An Kafa Cibiyar Kiwon Lafiya Ta Hadin Gwiwa Ta Farko Tsakanin Sin Da Afirka A Guinea

November 13, 2025
Jiga Jigan APC Sun Ziyarci Majalisar Wakilai Bayan Sauya Sheƙar Ƴan NNPP 2

Jiga Jigan APC Sun Ziyarci Majalisar Wakilai Bayan Sauya Sheƙar Ƴan NNPP 2

November 13, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.