A ranar Asabar ne kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) ya ce, aikin bututun iskar gas da ya fito daga Ajaokuta, Kaduna zuwa Kano (AKK) wanda aka kammala kashi 80 cikin 100, zai kammala baki daya a watan Disambar shekarar 2024.
Babban jami’in kamfanin NNPCL Mele Kyari, ya bayyana hakan a lokacin da ya ziyarci kashi na biyu na aikin – kogin Hadejia HDD da wani kamfanin dan kwangila mai suna BRENTEXCCP Limited ya kammala.
- ‘Yansanda Sun Ceto Mutum 4 Da Aka Sace A Jihar Katsina
- Matsaloli 15 Da Aikin Koyarwa Ke Fuskanta A Nijeriya
Kyari, wanda ya samu wakilcin mataimakin shugaban hukumar samar da iskar gas da makamashi ta NNPC, Olalekan Ogunleye, ya yabawa kamfanin kan yadda suka yi aiki tukuru bisa lura da kiwon lafiya na tsawon sa’o’i miliyan 7.2 ba tare da bata lokaci ko jin wani rauni ba.
A nasa bangaren, mataimakin shugaban kamfanin BRENTEXCCP Limited, Sani Abubakar, ya bada tabbacin cewa duk kayan aikin da ake bukata an tanada kuma a shirye suke domin cika wa’adin da aka gindaya musu.
Hukumar kamfanin mai na kasa NNPCL ta ce, aikin bututun iskar gas na AKK wani shiri ne da zai kara zurfafa dunkulewar yankin Arewacin kasar nan da yankin Neja Delta da sauran sassan kasar nan baki daya.