Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, a jiya ya ce, ‘yan kwangilar da ke gudanar da aikin hanyoyin Kano zuwa Zariya da na Zariya zuwa Kaduna tare da aikin Gadar Neja na 2 za su kammala tare da mikasu a ranar 15 ga watan Mayun 2023.
Ya shaida hakan ne ga ‘yan jarida bayan kammala zaman Majalisar zantawar ta kasa (FEC), tare da cewa, shi ma aikin babban hanyar Legas zuwa Ibadan mai nisan kilomita 116 tare da manyan gadojinsa zai kammala kuma za a mika wa gwammati shi zuwa ranar 30 ga watan Afrilu.
Sannan, ya ce, an amince da fitar da naira biliyan 1.39 domin farfado da kwangila da nufin kammala shi na Gadar Uto karo na biyu mai nisan kilomita 2.6 a Ikenje da ke jihar Delta daga naira biliyan 4.435 zuwa biliyan 5.835.
Ya ce, “Aikin Gadar Loko-Oweto tunin aka kammala shi. Shi ma Gadar Ikom an kammala. Sakatariyar Gwamnatin tarayya a jihohin Nasarawa, Bayelsa da Zamfara da na Awka an kammalasu su din ma, kazalika, rukunin gidajen Zuba, da gidaje 700 sun zama a kimtse ko yanzu za a iya kaddamar da su,” ya kara da cewa.
Shi kuma ministan noma da raya karkara, Muhammad Abubakar, ya ce, bukatar gina shalkwatar ma’aikatar noma da bunkasa yankunan karkara na gwamnatin tarayya ya samu amincewa.
A cewarsa, ana son a karon farko za a kashe naira biliyan 6 domin fara gudanar da aikin sabuwar Shalkwatar.
Abubakar ya ce, an tsara cewa ginin Shalkwatar mai hawa 10 za a kirasa da suna gidan noma.
Dangane da hauhawar farashin shinkafa, ya ce ana yin abubuwa da yawa don tabbatar da samun shinkafar da tabbatar da wadatuwarsa a cikin kasa, don kara rage farashinsa da saukinsa “Tun da Nijeriya ce ta daya a nahiyar Afirka wajen noman shinkafa.”