Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umurnin kara kashi 10 cikin 100 na kasafin kudi a bangaren harkokin kiwon lafiya.
Mai bai wa shugaban kasa shawara a fannin harkokin lafiya, Dakta Salma Ibrahim-Anas, ita ce ta bayyana hakan a wurin taron harkokin kiwon lafiya da ya gudana a Abuja.
Ta ce shugaban kasa yana da aniyar kara kasafi mai tsoka a bangaren harkokin lafiya a cikin kasar nan, domin inganta wannan fannin lafiya a Nijeriya.
“Tun kafin mu bai wa shugaban kasa shawara ya kara kasha 10 cikin 100 a fannin harkokin lafiya, kuma wannan somintabi ne.”
Ta kara da cewa wannan karo zai yi matukar tallafa wa fannin ta yadda za a gyara harkokin kiwon lafiya a Nijeriya.