A yau Alhamis ne ofishin zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin da ofishin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar sun sanar da cewa, za a kira taro na farko na majalisar wakilan jama’ar kasar karo na 14 a ranar 5 ga watan Maris dake tafe, kuma za a kira taro na farko na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa karo na 14 a ranar 4 ga watan Maris mai zuwa, inda za a samar da hidima mai inganci ga manema labarai na kasar Sin da na kasashen ketare bisa ruhin gaskiya ba tare da rufa rufa ba. (Mai fassarawa: Jamila)
Talla