Tsohon Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA), Sepp Blatter, da tsohon shugaban UEFA, Michel Platini, za su sake gurfana a gaban wata kotu a Switzerland kan zargin cin hanci da rashawa.
Kotun ɗaukaka ƙara da ke Muttenz za ta saurari buƙatar ofishin babban mai shigar da ƙara na ƙasar, wanda ke son sake dawo da tuhume-tuhumen da ake yi wa Blatter, mai shekaru 89, da Platini, mai shekaru 69.
Blatter ya ce yana fatan kotun za ta tabbatar da sahihancin kwantiragin da ke tsakaninsa da Platini, kamar yadda wata kotu ta yi a shekarar 2022, lokacin da aka wanke su daga zargin cin hancin dala miliyan 2.1.
Blatter ya shugabanci FIFA daga 1998 zuwa 2015, kuma an yi tsammanin Platini ne zai gaje shi kafin shari’ar ta hana shi ci gaba da neman shugabancin hukumar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp