A gobe Laraba ne za a wallafa makalar babban sakataren kwamitin kolin JKS, kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping, don game da kiransa ga dimbin miliyoyin ma’aikata Sinawa, na su zage damtse wajen shiga aikin ginin kasa mai karfi, da kara farfado da kasa.
Makalar ta shugaba Xi, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin soja na tsakiyar kasar ta Sin, za a wallafa ta ne cikin mujallar Qiushi ta 9 ta shekarar da muke ciki, wadda muhimmiyar mujjala ce ta kwamitin kolin JKS. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp