Za a wallafa makalar da babban sakataren kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping ya rubuta, game da ci gaba da aiki da karfin ruhin da aka samu a lokacin yakin turjiya ga zaluncin Japanawa a bisa hanyar neman farfado da kasa a mujallar Qiushi, wacce take babbar mujalla ta kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin.
Yakin shi ne mafi tsawo kuma mafi girma da jama’ar kasar Sin suka yi da zaluncin kasashen waje a wannan zamanin, wanda ya zo da mafi girman sadaukarwa, amma ya kai ga nasarar farko da Sinawa suka samu wajen ‘yantar da kasa. Har ila yau, nasarar yakin ta kasance wani muhimmin sashe na nasarar da duniya ta samu a kan mulkin danniya.
Kazalika, makalar ta yi nuni da cewa, sakamakon nasarar da aka samu ta yakin turjiyar jama’ar kasar Sin a kan zaluncin Japanawa da yaki da mulkin danniya a duniya ya zarce batun sabani kawai, kana ta ce, al’ummar kasar Sin da sauran al’ummomin duniya ba za su taba amincewa da duk wani yunkuri na musantawa, ko gurbata gaskiya, ko shafa fenti a kan tarihin mamayar ba.
Ruhi mai karfi da aka samu a lokacin yakin turjiyar ya kasance wani muhimmin ginshiki mai karfi, wanda ya jagoranci jama’ar kasar Sin zuwa shawo kan wahalhalu da cikas a yunkurinsu na farfado da kasa, kamar yadda makalar ta bayyana. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp