A yayin ziyarar aiki da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai kasar Malaysia, daga yanzu manyan kafofin sadarwa kamar kafar yada labarai ta kasar Malaysia za su fara nuna shirin bidiyon “Bayanan magabata dake jan hankalin Xi Jinping” na harshen Malay wanda CMG ya shirya.
Shirin ya mai da hankali ne kan muhimman batutuwa kamar gina al’umma mai kyakkyawar makomar bai daya ga bil Adama, da gadan al’adun gargajiya da kirkire-kirkire, da kare nau’ikan halittu, da mu’amala da koyo a tsakanin al’ummomi, ya kuma gabatar da fitacciyar hikimar shugaba Xi Jinping wajen gudanar da mulkin kasar. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)