A yayin ziyarar aiki da shugaban kasar Sin Xi jinping zai kai kasar Faransa, an fara watsa dandano da faifan bidiyon tallar “Labarun da Xi Jinping ya fi so” da babban rukunin gidajen radiyo da talabijin na kasar Sin CMG ya shirya musamman domin masu kallo na ketare, a wasu kafofin watsa labarai na kasar Faransa, kamar daily Motion da sauransu, daga ranar 2 ga Mayu agogon wurin.
Shirin “Labarun da Xi Jinping ya fi so” ya kunshi jerin zababbun labarai da kalamai da Xi ya ambata a cikin muhimman jawabai, da rubuce-rubuce da ya gabatar, inda a bayyane suka nuna hikimar siyasa da zurfin ilimin tarihi da na al’adu na shugaba Xi, tare da yin bayani mai zurfi game da ma’anoni da dabi’u na gama-gari wadanda ke kunshe a cikin kyawawan al’adun Sinawa. (Mai fassara: Yahaya)