Za a fara watsa shirin talabijin na musamman mai mai taken “Karfin Al’adu – Tushe da Aikace-Aikacen Tunanin Al’adu na Xi Jinping a Zhejiang”, ta kafar tashar telabijin ta CCTV-1 ta kamfanin CMG, daga yau Laraba 6 ga watan Agustan nan. Za a rika watsa shiri daya duk rana, daga shirin mai jimillar kaso hudu.
A lokacin da Xi Jinping ya yi aiki a Zhejiang, kafin ya zama shugaban kasar Sin daga bisani, ya jagoranci ci gaban bangaren al’adun yankin, ta yadda aka samu nasarori masu ma’anar tarihi. Wadannan nasarori sun ba da gudummawar gaske ga habaka tunanin al’adu na Xi Jinping, ta fuskar ka’idoji da kuma aikace-aikace. Shirin ya mayar da hankali kan wannan tsari na tarihi, wanda ke bayyana zurfin fahimtar Shugaba Xi game da muhimmancin aikin raya al’adu. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp