Yayin da aka shiga kakar noman auduga a jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta, dake arewa maso yammacin kasar Sin, manoman yankin za su yi amfani da na’urorin girbi na zamani, wajen cirar kaso sama da 80 bisa dari na audugar da aka noma bana a jihar.
A cewar sashen lura da ayyukan noma da raya karkara na jihar, an shirya amfani da na’urorin girbi sama da 7,000, domin gudanar da wannan aiki a kakar ta bana. Sashen ya kara da cewa, adadin audugar da aka noma a bana ta haura ta shekarar bara, yayin da kuma aka yi nasarar kara inganta fasahohin noman auduga a jihar.
Fannin noman auduga da masana’antun sarrafa ta, na kan gaba a fannin bunkasa tattalin arzikin jihar ta Xinjiang, inda sashen ya samar da jimillar tan miliyan 5.13 na auduga a shekarar 2021, adadin da ya kai kaso 89.5 bisa dari, na jimillar audugar da aka noma a daukacin kasar. (Saminu Alhassan)