A yanzu haka, siyasar Jihar Kano ta dauki dumi da kuma wani salo a kafafen sada zumunta kan wata sabuwar waka da fitattacen mai yi wa shugaban kasa waka, Dauda Kahutu da aka fi sani da Rarara ya yi wa gwamnan Kano, Abdullahi Umar gugar-zana.
Kafin dai wannan wakar ta gugar zana da Rarara ya yi wa Ganduje, a baya ya kasance daya cikin mawakan da ke a kan gaba wajen rera wa Ganduje wakokin goyon baya na siyasa, mussaman wacce ya yi wa Ganduje a lokacin zabukan 2015 da 2019.
- An Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Yawan Yanka Jakuna
- Hisbah Ta Cafke Karuwai 25 Da Masu Sayar Da Barasa 6 A Jigawa
An ruwaito cewa, Rarara ba ya goyon bayan tsaya wa takarar da mataimakin gwamnan Jihar, Nasiru Yusuf Gawuna ya yi a jam’iyyar APC, inda Rarara ya gwammace ya goyi bayan takarar Sha’aban Ibrahim Sharada na jam’iyyar ADP.
Sai dai, Rarara ya ce, har yanzu shi dan APC ne kuma ya na goyon bayan takarar Tinubu da Shettima.
Rarara a cikin sabuwar wakarsa da ta fita a ranar Laraba, wacce ya wake Tinubu da Shettima, wakar ta tabbatar da rikicin da ke a tsakanin Rarara da Ganduje, inda a cikin wakar, ya danganta Ganduje da wasu sunaye na haibaici.
Ya kuma soki Ganduje kan kin mika sunansa ga kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC.
Wannan sabuwar waka ta janyo mutane da dama sun furta albarcin bakinsu, inda wasu suka ce, fada ne na cikin gida, wasu suka ce, halin Rarara ne ya yi wa duk wanda ra’ayinsa bai zo daya da na sa ba, domin ko a baya, ya yi wa Malam Ibrahim Shekarau da Sanata Kwankwaso gugar zana iri-iri a cikin wasu wakokinsa.