Yau na ga wannan labari: Charles Onunaiju, wani masanin ilimin huldar kasa da kasa na Najeriya, ya ce asusun tarayyar Amurka na ci gaba da kara kudin ruwa, matakin da ke iya haifar da mummunan tasiri ga kasashe masu tasowa.
Don neman shawo kan matsalar hauhawar farashin kayayyaki, asusun tarayyar Amurka ya kara kudin ruwa har sau 6, tun farkon shekarar 2022.
Amma me ya sa matakin ya shafi sauran kasashe? Saboda wannan manufar za ta janyo dalar Amurka daga kasuwannin kasa da kasa, don su koma kasar Amurka. Hakan kuma zai sa a dinga canza kudaden sauran kasashe zuwa dalar Amurka, lamarin da zai haddasa faduwar darajar kudaden, da hauhawar farashin kayayyaki a wadannan kasashe, da karancin dalar Amurka, da jarin waje a kasuwanninsu, gami da raguwar adadin kayayyakin da suke fitarwa zuwa kasashen waje.
Don tinkarar wannan mummunan tasiri, manyan bankunan sauran kasashe su ma sun daga kudin ruwa don neman kiyaye dalar Amurka a gida. Misali, babban bankin Najeriya ya riga ya daga kudin ruwa zuwa 16.5%. Sai dai manufar ba ta yi amfani sosai ba, ganin yadda darajar Naira na ci gaba da raguwa. A sa’i daya kuma, karuwar kudin ruwa na haifar da karin matsin lamba ga kamfanonin da suka ci bashi daga bankuna.
A cewar Charles Onunaiju, yanzu Nijeriya na fama da hauhawar farashin kayayyaki da matsalar karancin dalar Amurka a kasuwa, da faduwar darajar kudin kasar da dai sauransu, galibi saboda yadda take fuskantar matsin lamba daga wasu manufofin kasashen ketare. Kana Najeriya da sauran kasashe masu tasowa na fuskantar matsalolin raguwar guraben aikin yi, da karuwar bashin da ake ci. Ta wata manufarta kadai, kasar Amurka ta tura matsalolin hauhawar farashin kayayyaki, da koma bayan tattalin arziki, ga sauran kasashe, musamman ma kasashe masu tasowa.
Matakan “kashin dankali” mai kama da wannan, da kasar Amurka ta yi wa sauran kasashe, sun yi yawa. Idan har mun dauki aminan kasar Amurka, wato kasashen Turai a matsayin misali. Ta hanyar fakewa da maganar daidaita yanayin da ake ciki a nahiyar Turai a fannin tsaro, kasar Amurka ta mai da kasashen Turai karkashin jagorancinta. Kana ta yi amfani da matsalar karancin makamashin da kasashen Turai suke fuskanta wajen sayar musu da iskar gas mai tsada matuka. Ban da wannan kuma, kasar Amurka ta ba da dimbin tallafi ga sana’ar kirkiro motoci masu amfani da lantarki ta kasar, don janyo masana’antun Turai zuwa gidanta. Ga shi, kasar ba ta kyautatawa aminanta, balle ma sauran kasashe.
A wannan zamanin da muke ciki, wata kasa kadai take samun dimbin tallafi daga kasar Amurka, wato kasar Ukraine. Amma dalilin da ya sa haka, shi ne Amurka na yin amfani da Ukraine wajen raunana kasar Rasha. An biya kudi, don sanya mutanen kasar Ukraine, maimakon na kasar Amurka zub da jini. Gaskiya Amurkawa suna da wayo.
Shafin yanar gizo ta Internet ta Modern Diplomacy, na Turai, ya ce kasar Amurka kasa ce dake son kwatar dukiyoyi daga sauran kasashe. Ko da yake wata babbar kasa ce, amma za ka yarda da manufarta ta “kashin dankali”?(Bello Wang)