Babban Hafsan Sojin Saman Nijeriya, Air Marshal Sunday Aneke, ya umarci kwamandojin rundunar da su ƙara tsananta hare-hare ta sama kan maɓoyar ‘yan bindiga a sassan ƙasar.
Aneke, ya bayyana haka ne yayin wani taro da ya jagoranta tare da manyan kwamandojin da ke kula da yaƙin da ake yi da ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga.
- An Kama Wani Mutum Kan Zargin Kashe Matarsa A Sakkwato
- Jirgin Ƙasa Ya Murƙushe Direban Adaidaita Sahu Da Fasinja A Jos
A taron, an tattauna sabbin dabarun da za a yi amfani da su wajen kai hare-hare, da kuma yadda rundunar za ta yi aiki tare da sauran hukumomin tsaro don samun nasara a yaƙin.
Sanarwar da rundunar sojin sama ta fitar bayan taron ta ce an cimma matsaya kan ƙarfafa haɗin kai tsakanin sojin sama, sojin ƙasa, da sauran hukumomin tsaro.
Wannan mataki ya biyo bayan mako guda da rantsar da sabbin hafsoshin tsaro da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi.













