Gwamnan Jihar Ribas da aka dakatar, Siminalayi Fubara, ya ce yana amfani da hanyoyin da doka ta tanada domin kare haƙƙinsa da na al’ummar jiharsa, duk da matsalolin siyasa da yake fuskanta.
A cikin wata sanarwa da ya fitar bayan dakatar da shi da mataimakiyarsa na tsawon watanni shida, Fubara ya ce tun daga lokacin da ya hau mulki, ya yi ƙoƙarin kare rayuka da dukiyoyin jama’a da kuma kawo ci gaba.
- ‘Yansanda Sun Kama Wata Mata Da Ake Zargi Da Safarar Makamai A Katsina
- WSCIJ Ta Naɗa Farfesa Umaru Pate A Kwamitin Amintattu
Sai dai, ya ce ‘yan majalisar dokokin jihar suna ta hana shi aiwatar da ayyukansa.
Ya bayyana cewa bayan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya shiga tsakani, ya gaggauta bin yarjejeniyar da aka cimma, ciki har da mayar da kwamishinonin da suka ajiye aiki.
Sai dai, duk da hakan, ya ce yana fuskantar cikas daga majalisar dokokin jihar.
Fubara ya ƙara da cewa, duk da rikicin siyasar da ake fama da shi, gwamnatinsa tana ci gaba da aiki yadda ya kamata, kuma ana biyan ma’aikata albashinsu tare da ƙaddamar da muhimman ayyuka a jihar.
Ya buƙaci al’ummar jihar su ci gaba da bin doka da oda, yana mai cewa za su ci gaba da tuntuɓar hukumomin da suka dace domin tabbatar da cewa dimokraɗiyya ta ci gaba da ƙarfafa a jihar.
An fara samun matsala a siyasar Jihar Ribas tun bayan da rashin jituwa ya ɓulla tsakanin Fubara da tsohon gwamnan jihar, wanda yanzu shi ne Ministan Birnin Tarayya, Nyesom Wike.
Rikicin ya kai ga cewa wasu ‘yan majalisar dokokin jihar masu biyayya ga Wike suka yi barazanar tsige Fubara daga muƙaminsa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp