Shugaban Rukunan Kamfanin Gerawa Group, mamallakin Kamfanin Sarrafa Shinkafar Gerawa, Alhaji Isa Muhammed Gerawa, ya bayyana aniyarsa ta ci gaba da gudanar da abubuwan da suka sa Kamfanin LEADERSHIP ya zabe shi domin ba shi lambar yabo a matsayin Gwarzon Dan Kasuwa na shekarar 2023.
Babban dan kasuwar ya bayyana haka ne yayin da tagawar mahukuntan Kamfanin LEADERSHIP bisa jagorancin Daraktan Ayyuka na Musamman, Mista Paul Agbo ta ziyarci ofishinsa da ke Abuja domin mika masa takardar ayyana shi a matsayin gwarzon dan kasuwa.
Ya bayyana godiyarsa bisa wannan karramawa, yana mai cewar, “Ina godiya kwarai da gaske ga mahukuntan Kamfanin LEADERSHIP bisa yadda kuka zabe ni a matsayin gwarzon dan kasuwa wanda kuka ga ya dace ku ba ni wata lamba ta girmamawa a kan harkokin kasuwanci kamar yadda kuke zubar mutane duk shekara ku karrama su, kuka zabe ni a matsayin dan kasuwa wanda ya ba da gudummawa musamman a kan harkar abinci wanda za ku ba da wannan lamba a watan uku.
“In Allah ya so ya yarda za mu zo da mutanenmu mu nuna godiya da kuma jin dadi bisa yadda kuka mutunta mu kuka ba mu lambar yabon, duk da cewa ba mu muka fi kowa ba a ‘yan kasuwar Nijeriya amma kuka ga mu ya dace bisa binciken da kuka yi, kuka ga meye dalilin da ya dace kuka ba da wannan lambar yabon, muna godiya kwarai da gaske.
“Kuma in Allah ya so ya yarda za mu ci gaba da yin abin da muke yi wanda ya sa kuka ga ya dace ku karrama mu da lambar yabon, muna godiya kwarai.” Ya bayyana