‘Yan kasuwa a Kano sun baiwa mazauna jihar tabbacin daidaita farashin kayan abinci da sauran kayan masarufi kafin watan azumin Ramadan.
‘Yan kasuwar sun bayyana haka ne jim kadan bayan wata ganawa da Shugaban Hukumar Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kano (PCACC), Barr. Muhuyi Magaji Rimin-Gado a ranar Litinin bisa zarginsu da boye kayayyakin abinci don tsammanin ya yi tsada su sayar.
- NLC Na Neman A Biya Ma’aikata Naira Miliyan Ɗaya A Matsayin Sabon Mafi Ƙarancin Albashi
- Bangaren Samar Da Kaya Ko Aiwatar Da Ayyukan Hidima Da Ma’aikatan Kamfani Ke Yi Ya Fadada A Kasar Sin A Shekarar 2023
In ba a manta ba, a ranar Lahadin da ta gabata, mun rahoto muku cewa, hukumar PCACC ta rufe wasu ma’ajiyar abinci guda goma da ake zargi da boye kayan abinci iri-iri a kasuwar hatsi ta Dawanau.
Da yake zantawa da manema labarai a madadin ‘yan kasuwar bayan ganawa da shugaban hukumar PCACC, daya daga cikin manyan dillalan kasuwar Singa, Alhaji Ibrahim Danyaro, ya ce za su yi aiki kafada da kafada da hukumar domin ganin an daidaita farashin kayayyakin abinci domin a samu saukin farashin don saukaka rayuwa ga al’ummar Kano da sauran mutane.