Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Hansi Flick, ya bayyana cewa kungiyarsa za ta je har gidan Atletico Madrid ta doke ta a wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin Coppa Del Rey, bayan da Barcelona da Atletico Madrid suka tashi 4-4 a wasan farko zagayen daf da karshe a Copa del Rey ranar Talata a filin wasa na Estadi Olimpic Lluis Companys.
Minti daya da fara wasan Atletico Madrid ta fara cin kwallo ta hannun Julian Albarez, sannan Griezmann ya kara ta biyu a minti na biyar Tsakani amma daga baya Barcelona ta zare daya ta hannun Pedri a minti na 19, sannan Cubarsi ya farke ta biyu minti uku Tsakani sannan kafin hutu Barcelona ta kara ta uku ta hannun Martinez, haka suka je zagayen farko Barcelona na cin 3-2.
- Noman Dabino: Jigawa Ta Yi Hadaka Da Saudiyya
- Yawan ’Yan Kasashen Waje Da Suka Shigo Kasar Sin Ba Tare Da Biza Ba A Bara Ya Ninku
Bayan da suka koma zagaye na biyu ne, sai Barcelona ta ci ta hudu a karawar ta hannun Lewandowski kai kace an tashi da Atletico Madrid a wasan amma daga baya kungiyar da Diego Simeone ke jan ragama ta zare kwallo ta uku ta hannun Llorente daga baya ta zare ta hudu ta hannun Sørloth dab da za a tashi daga wasan wanda yaja hankalin ‘yan kallo a duniya.
Wannan shi ne karo na biyu da suka kece raini a tsakaninsu a bana, bayan da Atletico ta je ta doke Barcelona a La Liga ranar 21 ga watan Disamba kuma a ranar Laraba 4 ga watan Afirilu, Atletico za ta karbi bakuncin wasa na biyu a daf da karshe a Copa del Rey. Barcelona ce ta daya a kan teburin La Liga da maki 54, iri daya da na Real Madrid ta biyu da kuma Atletico mai maki 53 ta ukun teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp