Assalamu alaikum, Malam, sau da yawa idan Kajinmu sun mutu mukan jefa wa kifi su cinyen mushen, shin ya halatta? Wa alaikum assalam.
A zahiri hakan ba daidai ba ne saboda an haramta cin mushe ne saboda manufofi Kamar haka:
1. Kasancewar ba a san cutar da ta kashe shi ba.
2. Dankarewar jini a cikin namanta, saboda ta mace kafin a yanka ta.
3. Allah ya bayyana cewa Mushe kazanta ne, kamar yadda ya zo a suratul An’am.
Don neman Karin bayani duba: Makasidush Shari’a indassa’ady shafi na: 302 Kasancewar jikin kifin yana ginuwa ne da abincin da yake ci, cin sa zai iya zama hadari ga rayuwar bil-adama, wannan ya sa ciyar da su da abinci mai kyau shi ne ya dace da Shari’a.
Duk wanda ya kyautata sana’arsa, Allah zai sanya masa albarka ya kuma habaka arzikinsa. Allah ne mafi sani.