Wata mata mai shekara 25 da mijinta ‘yan kasar Mali sun haifi ‘ya’ya tara, a wani asibitin kasar Maroko, lamarin da ya karya tarihin Kundin Tarihi na Duniya na yawan ‘ya’yan da aka taba haifa a lokacin haihuwa kuma har yanzu suna rayuwa.
Matar da ta haihu mai suna Halima Cissé, ‘yar shekara 25, ta sa likitoci biyu sun duba ta a lokacin da take da juna biyu don tabbatar da ko tana dauke da ‘ya’ya lamarin da ya bar su cikin mamaki.
Bayan tabbatar da adadin yawan ‘ya’yan, gwamnatin Mali ta kai ta ita da mijinta zuwa Maroko don likitoci su kula da ita yadda ya kamata.
A 2021 Halima ta haifi yaranta guda tara reras, maza biyar mata hudu, kuma kowannensu yana cikin koshin lafiya, sannan ita kanta tana cikin matukar farin ciki da wannan babbar kyauta da ta samu.
A cikin wata hira da mijinta ya yi da BBC, y ace jariran baki daya suna cikin koshin lafiya.
Matar daga Afirka ta Yamma ta doke tarihin da wata mata ta taba kafawa na haihuwar yara takwas ragas, wanda dukkansu na raye.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp