Injiniya Abubakar Ibrahim Musa matashi ne a Jihar Bauchi da ke arewacin Nijeriya, wanda ya kware wajen hada Sola Panels, wato faranti mai amfani da haske rana ya mayar da shi zuwa lantarki da sauran abubuwan kere-kere, ya shaida cewar ta hanyar kera Farantin nan za a iya samar wa dubban ‘yan Nijeriya ayyukan yi.
Abubakar wanda ke da mallakin kamfanin Kuantun Engineering DPS da ke Jihar Bauchi sun kware a bangaren kere-keren abubuwan da suka shafi na solar Panels da sauran abubuwan da ake sarrafa su domin bayar da wutar lantarki daga hasken rana.
- ‘Yan Bindiga Sun Sace Matafiya A Babbar Hanyar Gusau-Funtua
- Nijeriya Na Asarar Dala Biliyan $1.5 Sakamakon Yin Bahaya A Fili
Injiniya Abubakar Ibrahim Musa da aka haifa a 1982 ya shaida cewar ya karanci ilimin fasaha a bangaren injiniyanci na hada kayan wuta wanda ya samu shaidar matakin karatun digiri na biyu yanzu na neman ya uku.
A binciken da wakilinmu ya gudanar kamfanin na kuma horas da matasa da dama kan harkokin da suka shafi injiniyanci na electrical engineering.
Kamfanin ya kware wajen hada Light Bulbs, Solar Panels, Solar Streetlights, Floodlight, Solar Generators da dai sauransu.
Matashin ya ce yana yin kwayayen lantarki da sauran abubuwan da suka shafi lantarki. Ya ce ya hada gwiwwa da wani kawunsa don kirkirar wannnan kamfanin samar da lantarki don tallafa wa al’umma da samar da ayyukan yi ga matasa.
Injiniya Abubakar ya ce wasu kayyakin aikin da suke amfani da su sukan sayo ne daga kasar China, yayin da wasun kuma a Nijeriyar suke samunsu.
Ya ce a kowace rana suna kirkirar solar Panels akalla 60. Ya ce babban kalubalen da yake fuskanta a yanzu shi ne rashin karfin jarin da zai bunkasa kasuwancinsa.
Abubakar ya bayyana cewar sun kirkiri kamfannsu ne lura da yanayin kukan matsin tattalin arziki da ake ciki a kasar nan da kuma rashin aikin yi a tsakanin jama’a.
Ya ce kamfanin nasu suna sarrafa abubuwa da yawa kamar su farantin wuta mai amfani da hasken rana ya maida shi zuwa wutar lantarki (Solar Panel), da kuma yin koyayen hasken wuta na zamani da turakun solar na kan layuka da wasu abubuwa na fasaha.
“Abubuwan da muke sarrafawa kamar shi faranti mai maida hasken rana zuwa wutar lantarki muna samun wasu kayan aikin da muke hadawa wasu kuma saimub shigo da su daga kasar China. Kamar abin da ya shafi Solar Cells da solar ribbon, wires su muna zuwa da sune daga kasar China. Amma irin su
Aluminium profile, glass da sauransu duk muna samu a nan Nijeriya.”
Ya tabbatar da cewar jama’a suna sayen kayansu amma suna bukatar manyan masu sayen da su karfafa musu guiwa wajen sayen abubuwan da suke sarrafawa.
Daga bisani ya yi korafin rashin jari, yana mai cewa harkar da suka shafi Solar suna nan birgik muddin aka dafa lallai za a samu guraben ayyukan yi ga dubban jama’a a Nijeriya da dama da rage dogaro da wutar lantarki a fannoni daban daban.
“Babban burin mu shi ne samar da ayyukan yi a tabbatar ayyuka sun samu a cikin kasa kuma an saukaka wa al’umma.”