A daidai lokacin da matsalolin tsaro ke kara ta’azzara a Nijeria, Gwamnatin Tarayya ta ce za ta sa kafar wando daya da barayin danyen man fetur da ke wadaka da shi ta barauniyar hanya.
Shugaba Muhammadu Buhari, ya ce gwamnatinsa za ta yi fito-na-fito da masu satar danyen man kasar, mako guda bayan da hukumomin Nijeriyar suka cafke wata tankar dakon mai ta barauniyar hanya a gabar tekun Guinea.
- ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Lauya A Zamfara
- Gwamnatin Nijeriya Na Kashe Naira Biliyan N18.397 Kullum A Bangaren Tallafin Mai
Shugaban ya ce ko kadan Nijeriyar ba za ta amince wasu bata-gari su dinga amfani da dimbin arzikin danyan man fetur din da kasar ke da shi yadda suka ga dama ba.
Saboda hakan ya umarci jami’an gwamnatinsa da su kawo karshen wannan matsala musamman ma a yankin Neja Delta da ke Kudu maso Gabashin kasar da kuma ke da arzikin man fetur din.
Nijeriyar dai na da bukatar hada kai da makwabtanta domin kawo karshen wannan matsalar cikin gaggawa, a cewar wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar.
Matsalar satar danyen man fetur abu ne da ke ciwo gwamnatin Nijeriya tuwa a kwarya, wanda ko gwamnatocin baya sai da suka yi yaki da masu fasa bututun man musamman a Neja Delta.