Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Mikel Arteta ya ce tabbas Arsenal tana bukatar sayo karin ‘yan wasa kafin fara kakar bana, idan har suna son lashe Premier League a kakar mai zuwa.
Kungiyar da Arteta ke jan ragama ta yi rashin nasarar lashe babban kofin gasar firimiya a Ingila a kakar wasa ta 2022 zuwa 2023, bayan da Manchester City ta sha gabanta daga baya.
Ana alakanta Arsenal da cewar za ta dauki dan wasan West Ham, Declan Rice ta kusan biyan kudin Kai Havertz da Chelsea ta sallama mata dan kwallon duka domin ganin ta lashe firimiya.
Arteta ya bayyana cewar kakar da za a fara ta nan gaba za ta zama mai tarin kalubale a tarihin Premier League domin kungiyoyi da dama za su shirya domin ganin sun ba wa marada kunya a gasar.
Arsenal ta dade tana jan ragamar teburin Premier League daga baya matakin ya sullube mata, bayan da wasu manyan ‘yan wasanta suka ji ciwo har da dan wasan baya, William Saliba.
Amma dai Arsenal ta kare a mataki na biyu a teburi, za kuma ta buga Champions League, amma Arteta ya ce lamarin ya kona musu rai kuma za su yi kokarin gyara kuskuren da suka yi.
Manchester City ce ta lashe Premier League a kakar da ta wuce na uku a jere kuma na biyar a kaka shida sannan kungiyar ta lashe FA Cup da Champions League, kamar yadda Sir Aled Ferguson ya dauki kofi uku a 1999 a Manchester United.
Ranar 6 ga watan Agusta za’a buga Community Shield tsakanin Manchester City da Arsenal a filin wasa na Wembley sannan mako guda tsakanin a fara wasannin satin farko a Premier League.