Daya daga cikin masu neman takarar shugabancin kungiyar Musabiha ta ‘yan kasuwar kofar Ruwa da ke Kano, Abdullahi Muhammad Bala ‘Yanleman ya bayyana dalilin fitowarsa takarar da cewa saboda ganin abubuwa daban-daban da ke faruwa a kasuwar na rashin ci gaba da koma baya da take fuskanta ta sa ya fito.
Ya ce takarar da ya fito ba na yin kansa ba ne, dattawan kasuwa da matasa da sauran masu kishi da son ci gaban kasuwar ne suka ga dacewar ya ba da gudunmuwa, ganin jajircewa da yake a kan ci gaban kasuwar wajen ba da gudunmuwa sosai idan ya zama shugaba.
Alhaji ‘Yanleman ya shaida wa ‘yan jarida cewa, “Akwai matsaloli da suke damun kasuwar da yawa, musamman vangaren harkar tsaro da ta addabi kasuwar matuka, domin sai ka rufe shago ka tafi gida ka dawo da safe ka ga an valle maka, wani lokacin har fasa bango ake a shiga a kwashe mana kaya,” in ji shi.
Ya ce yana daga cikin babban burinsa ya kyautata tsaron kasuwa da alaka da gwamnatin Jihar Kano domin a zo a rika yi musu ayyuka na ci gaba, kama daga gyaran hanyoyi da samar musu da rijiyoyin burtsatse da kuma sanya musu fitilu da za su haskaka kasuwar wajen taimaka wa harkar tsaro.
‘Yanleman ya yi nuni da cewa kungiyar tasu ta yi shugabanni da yawa tun daga kan Alhaji Mati da Alhaji Tukur, wanda daga kansa shugabanni da suka biyo baya babu abin da suka kawo wa kasuwar na ci gaba.
Ya ce, “Komai ka gani ya gyaru ko ya lalace a gida daga mai gida ne. Yanzu muna duba yaya za a yi mu zo mu hada kai don gyara kasuwar, domin kasuwa tana da albarka da daraja, sannan komin dare ka zo za ka sami abin da za ka ci abinci da kai da iyalinka ballanta ma kana da abin yi, ba kamar sauran kasuwanni ba,” ya jaddada.
Ya kara da cewa kasuwar tana da tarin matasa da dimbin albarka, amma shugabanni da suka gabata da ba su da manufofi masu kyau, amma su sun shigo da manufofi masu kyau na neman wannan takara in suka yi nasara za su yi abin da za su bar tarihi ta inganta ci gaba.