Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas, ya yi barazanar taimakawa wajen sa wa jam’iyyar PDP ta fadi zaben shugaban kasa a 2023.
Wike, wanda yake takun saka da Sanata Iyioricha Ayu, shugaban jam’iyyar PDP na kasa, ya bayyana haka ne a wajen kaddamar da wata hanya a unguwar Omerelu da ke karamar hukumar Ikwerre ta Jihar Ribas, ranar Alhamis.
- Bikin Baje Kolin Cinikayyar Hidimomi Na Kasa Da Kasa Ya Shaida Fatan Kasar Sin Na Cimma Moriyar Bai Daya
- ‘Yan Bindiga Sun Yi Wa Sojoji Kwanton Bauna, Sun Kashe Sojoji 2 A Katsina
Gwamnan, ya mayar da martanin ne kan kalaman da Ayu ya yi a kwanakin baya na cewa wadanda ke neman ya sauka daga mulki yara ne.
A wata hira da BBC Hausa, Ayu ya ce, “Ban taka wata doka ba; a gaskiya ina kokarin kawo gyara a jam’iyyar. Ni da gaske ban damu da rigimar da ba dole ba. Lokacin da muka fara tafiyar PDP, yaran nan ba sa nan. Yara ne da ba su san dalilin kafa jam’iyyar ba. Ba za mu bari wani mutum ya hargitsa jam’iyyarmu ba.”
Amma a martanin da ya mayar, Wike ya bayyana Ayu a matsayin mutum mai kwadayi .
Ya ce a fili yake cewa Ayu yana son PDP ta fadi a 2023 kuma a shirye yake ya taimaka masa ya cimma hakan.
Wike na ci gaba da yin takun saka da tsagin dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar da kuma shugabancin jam’iyyar tun bayan faduwa zaben fidda-gwanin jam’iyyar.