Shugaban Hukumar Yaki da masu yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annuti (EFCC), Abdulrasheed Bawa, ya ce, har yanzun akwai sama da Naira biliyan 500 da ‘yan siyasa suka boye, ba su koma babban bankin Nijeriya (CBN) ba.
Abdulrasheed Bawa ya bayyana haka ne a wata hira da gidan talabijin na Channels TV a wani shiri mai taken ‘Siyasa a yau’.
Shugaban na EFCC ya kara da cewa, hukumar na da bayanai da dama kan wasu hanyoyin da ‘yan siyasa ke tsarawa na sayen kuri’u a lokacin zabe.
Ya ce, “Zabin da ya rage wa ’yan siyasa kadai a yanzu shi ne, su siya kuri’u, domin na’urar BVAS za ta bayar da mamaki da yawa.”
Wannan shi ne bayanin sirrin da muke da su, kuma ina farin ciki da cewa dukkan hukumomin tsaro sun dukufa wajen ganin an gudanar da zaben cikin nasara.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp