Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammad ya samu nasarar lashe akwatin mazabarsa a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar Asabar.
Jam’iyyar PDP dai ta samu nasara da kuri’u 103 a rumfar zabe ta Bakin Dutse da ke Yalwan Duguri a karamar hukumar Bauchi, yayin da jam’iyyar APC ta samu kuri’u 25 kacal.
- An Cimma Tudun Dafawa Wajen Karfafa Hadin-Gwiwar Sin Da Afirka
- Zaben 2023: Atiku Ya Lashe Akwatin Mazabar Gwamnan Gombe
Kazalika, a zaben kujerar Sanata a wannan rumfar PDP ta samu kuri’a 101; APC kuri’a 32; NNPP kuma ta samu kuri’a 17 kacal.
A zaben dan majalisar wakilai da na tarayya; PDP 82 ta samu kuri’u; APC ta samu 65; NNPP kuma kuri’a biyar.
A mazabar Yalwan Duguri kuwa, Atiku ya samu nasara da kuri’a 103, yayin da Tinubu na APC ya samu kuri’u 25 kacal.
A zaben Sanata, PDP -101; APC – 32; NNPP kuma kuri’a 17.
A zaben majalisar tarayya, PDP – 82; APC 65; NNPP biyar.