A ranar Lahadin nan INEC ta bude cibiyar tattara sakamakon zaben shugaban kasa ta kasa domin bayyana sakamakon zaben shugaban kasa na 2023.
An bude cibiyar ne da misalin karfe 1 na rana sabanin karfe 12 na rana sabanin yadda shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya sanar a ranar Asabar.
- Zaben 2023: Wasu ‘Yan Bindiga Sun Sace Ma’aikatan INEC 3 A Taraba
- INEC Ta Dage Zaben Shugaban Kasa Da Na ‘Yan Majalisun Tarayya Zuwa Yau Lahadi A Yenagoa
A halin yanzu, cibiyar tana dauke da tawagar masu sa ido kan zabe da suka hada da kwamishinonin INEC na kasa da sufeto janar na ‘yan sanda, Usman Alkali, da ‘yan jarida da wakilan jam’iyya da dai sauransu.
A halin yanzu, Farfesa Yakubu, ya karanto hanyoyin gudanar da yadda abun zai kasance a matsayinsa na babban jami’in kula da masu kada kuri’a na tarayya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp