Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ya lashe akwatin mazabar gidan Sarkin Kano da kuri’a 99 a zaben shugaban kasa, yayin da APC mai mulki ta samu kuri’a 39.
A zaben Sanata da aka gudanar a mazabar ta gidan Sarkin Kano, jam’iyyar NNPP ta samu kuri’a 102, APC ta samu kuri’a 53 yayin da kuma jam’iyyar PDP ta samu kuri’a 15.
- 2023: Atiku Ya Lashe Wani Akwati Da Ke Cikin Gidan Gwamnatin Jihar Kaduna
- Zaben 2023: ‘Yan Daba Sun Sace Na’urar BVAS 8 A Delta Da Katsina
A zaben ‘yan majalisar tarayya kuwa, NNPP ke kan gaba da kuri’a 99, sai APC ke biye mata da kuri’a 46, PDP ta samu kuri’a 24, yayin da jam’iyyar ADC ta samu kuri’a hudu kacal.
A yanzu haka dai ana ci gaba da tattara sakamakon zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya da aka gudanar a yau Asabar.