Wasu ‘Yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun yi garkuwa da ma’aikatan wucin gadi uku na hukumar zabe ta kasa (INEC) a karamar hukumar Donga a jihar Taraba.
An yi garkuwa da su ne da yammacin ranar Asabar a lokacin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya na 2023.
- Yadda Jami’an EFCC Suka Yi Dirar Mikiya A Rumfunan Zabe A Zamfara
- Mai Juna Biyu Ta Rasu A Runfar Zabe A Jihar Zamfara
Ko’odinetan Cibiyar Tallafawa Zabe (EOSC) da ke hedikwatar INEC a jihar, ya tabbatar da sace ‘yan matan, ya ce sun samu rahoton faruwar lamarin daga jami’in zabe na karamar hukumar Donga.
Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Usman Abdullahi ta wayar tarho, ya ce har yanzu rundunar ba ta samu rahoton faruwar lamarin ba.